A cewar rahoton wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga Kashan, Hujjatul Islam Muhammadreza Islami-Tabar ya bayyana a daren Juma’a, a zaman tafsirin aya ta 26 ta Suratul Isra’i da aka gudanar a Masallacin Ayatullah Razavi na wannan gari, cewa: wajen bai wa wasu hakkinsu da kyautata musu, kada a taba bin zuciya da ji kawai, kuma kada a yi wuce gona da iri ko sakaci.
Ya kara da cewa: "Kalmar "tabzir" (barnatarwa) galibi ana amfani da ita ne da ma’anar watsa dukiya ko almubazzaranci a harkokin kudi. Wani lokaci mutum kan kashe dukiyarsa a hanya mai kyau, amma ya wuce ƙima; misali a lokacin liyafa yana amfani da dukiya ta hanyar da ta dace, amma wani lokaci sai a samu wuce gona da iri da almubazzaranci ko israfi a irin wannan amfani, kuma wannan ma ɓarna ce."
Limamin Juma’a na wucin gadi a Kashan ya ci gaba da cewa: "Wani lokaci almubazzaranci tana bangaren kuɗi, wato mutum ya kashe dukiyarsa a hanyar da ba ta dace ba kuma haramun ce, ko ya kashe abin da ya samu da wahala a hanya marar kyau; wannan ma wani nau’i ne na almubazzaranci."
Ya bayyana cewa wani lokaci kuma ɓarna tana bayyana a abubuwan da ba na kudi ba, yana mai tunatarwa cewa: "Gaba ɗaya, ɓata kowace ni’ima almubazzaranci ne, kuma duk wanda ya bata ni’imar rayuwarsa da kuruciyarsa, to ya aikata almubazzaranci."
Hujjatul Islam Islami-Tabar ya ce: "Mutum na iya amfani da ni’imar harshe da ido da kunne da hannu da kafa wajen samun ladan lahira, haka kuma yana iya amfani da wadannan ni’imomin Allah a hanyar zunubi da saɓawa a Allah. Saboda haka, bata ni’imomin Allah shi ma wani nau’i ne na almubazzaranci."
Ya bayyana cewa ba wa mutanen da ba su dace ba masa'uliyya yana daga cikin nau’o’in ɓarna, yana mai cewa idan aka ba jahilai mukamai da jagorancin kasa maimakon masu ilimi da nagarta, wannan misali ne na ɓarna. Ya kara da cewa: "Ba wa jahilai da marasa cancanta jagoranci yana sa damar yi wa jama’a hidima ta lalace a banza."
Hujjatul Islam Islami-Tabar ya yi nuni da tafsirin aya ta 27 ta Suratul Isra’i, yana mai cewa: "A haƙiƙanin gaskiya, aya ta 27 tana bayanin dalilin jumlar da ta gabata ne, tana hani da almubazzaranci, har ma tana bukatar mutum kada ya bi ji da zuciya kawai ko da a cikin kyautata wa wasu.
Ya kuma ce: "Allah Ya sanya hankalin mutum a saman jikinsa, wato a kai, domin hankali ya zama mai mulki a kan dukkan jiki. Saboda haka dukkan motsinmu da halayenmu su kasance masu bin jagorancin hankali. Kuma hankali wani karfi ne da ake bautar Allah da shi, kuma ta hanyarsa ne ake samun Aljanna."
Ra'ayinka